Hukumomi a Kano sun amince da mafi ƙarancin sadakin aure Naira dubu 20
Daga Jameel Lawan Yakasai
Hukumar zakka da hubusi ta jihar Kano tare da hukumar shari’a da majalisar malamai da ƙungiyar limaman masallatan Juma’a da ƙungiyar ma’aikatan zakka da waƙafi ta ƙasa sun amince da sabbin ka’idoji kan nisabin zakka, diyyar rai dasadakin Aure a jihar.
A taron da aka gudanar a Kano ranar Alhamis, an yanke shawarar amincewa da Naira dubu 20 a matsayin mafi ƙarancin sadakin aure, Naira miliyan 150 a matsayin diyya ga wanda aka kashe bisa kuskure da kuma naira dubu 985 a matsayin nisabin zakka, bisa lissafin farashin Durham.
KU KUMA KARANTA: Hukumar zakka da waƙafi ta raba kayayyakin jin ƙai ga marasa galihu a Zamfara
Babban sakataren ƙungiyar ma’aikatan zakka da wakafi ta kasa, Farfesa Aliyu Dahiru Muhammad na jami’ar Bayero Kano ne ya bayyana cewa taron ya kuma amince a ci gaba da gudanar da irin wannan zama duk bayan wata uku domin dubawa da sabunta wadannan ka’idoji.
Haka kuma, an tsara a sanar da gwamnatin jihar domin shirya taron wayar da kai tare da ƴan jarida da kuma isar da sakonni ta hanyoyin da suka dace.









