Tinubu ya naɗa Pedro a matsayin sabon shugaban gidan talabijin na ƙasa, NTA

0
165
Tinubu ya naɗa Pedro a matsayin sabon shugaban gidan talabijin na ƙasa, NTA
Rotimi Pedro sabon shugaban gidan talabijin na ƙasa, NTA

Tinubu ya naɗa Pedro a matsayin sabon shugaban gidan talabijin na ƙasa, NTA

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi babban sauye-sauye na shugabanci a gidan talabijin na ƙasa (NTA), inda ya naɗa Rotimi Richard Pedro, a matsayin sabon Darakta-Janar na gidan talabijin din na gwamnati.

“Sauran manyan nade-naden sun haɗa da Karimah Bello daga Jihar Katsina a matsayin Daraktar Tallace-Tallace, Stella Din daga Jihar Filato a matsayin Daraktar Labarai, da kuma Sophia Issa Mohammed daga Jihar Adamawa a matsayin Babbar Darakta ta Kamfanin NTA Enterprises Limited.

KU KUMA KARANTA: A gaggauta sakin Jamila Ibrahim da jaririnta – Amnesty International

“Pedro, ɗan asalin Legas, fitaccen mai kasuwanci a fannin kafafen watsa labarai da kuma mai ba da shawara, wanda ke da kusan shekaru talatin na kwarewar jagoranci a harkar watsa shirye-shirye, wasanni, da kuma tallace-tallace a faɗin Afirka, Birtaniya da Gabas ta Tsakiya,” in ji sanarwar.

Leave a Reply