Har yanzu ba mu ga dala dubu 100 da Tinubu ya yi mana alkawari ba – Kaftin ɗin Super Falcons

0
358
Har yanzu ba mu ga dala dubu 100 da Tinubu ya yi mana alkawari ba - Kaftin ɗin Super Falcons

Har yanzu ba mu ga dala dubu 100 da Tinubu ya yi mana alkawari ba – Kaftin ɗin Super Falcons

Daga Jameel Lawan Yakasai

Kyaftin din Super Falcons, Rasheedat Ajibade, ta bayyana cewa har yanzu tawagor ba ta karɓi kyautar dala $100,000 da aka yi musu alkawari ba, tare da wasu sauran alƙawuran da Gwamnatin Tarayya ta yi bayan nasarar da suka samu a Gasar Cin Kofin Mata ta Afirka (WAFCON) ta 2025 a Morocco.

A wata hira da Chude Jideonwo, Ajibade ta nuna rashin jin daɗi game da jinkirin biyan kuɗin.

Chude ta tambaye ta: “Sun baku dala $100,000 ɗin?”

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya baiwa ‘yan wasan Super Falcons kyautar lambar girma ta ƙasa da dala dubu 100 ga kowace ‘yar wasa

“Muna nan ba mu karɓi kuɗinmu ba, amma muna fatan za a biya. Ba su cika duk alƙawuran ba; ba mu karbi komai ba,” in ji ta.

Ajibade ta jagoranci Super Falcons ta samu nasarar lashe gasar a Morocco, inda suka lashe kofin WAFCON karo na 10 a tarihi.

Leave a Reply