Gwamnatin tarayya ta dakatar da samar da sabbin jami’o’i a ƙasar 

0
179
Gwamnatin tarayya ta dakatar da samar da sabbin jami'o'i a ƙasar 

Gwamnatin tarayya ta dakatar da samar da sabbin jami’o’i a ƙasar

Daga Jameel Lawan Yakasai

Majalisar zartarwa ta ƙasa, karkashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a ranar Laraba ta amince da dakatar da kafa sababbin makarantun gaba da sakandire na tarayya a duk faɗin ƙasar na tsawon shekaru biyar.

Dakatarwar ta shafi jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha (polytechnics), da kuma kwalejojin ilimi.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a yayin zaman majalisar.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya canza sunan Jami’ar Maiduguri zuwa Jami’ar Muhammadu Buhari

Alausa ya bada dalilan wannan mataki da cewa babban ƙalubale a fannin ilimi a Najeriya yanzu ba samun damar shiga makarantu ba ne, illa magance yawaitar kafa sababbin makarantun da dama can akwai su.

A cewar sa, hakan ya janyo tabarbarewar ilimi ta hanyar ƙarancin gine-gine da ma’aikata.

“Idan ba mu ɗauki mataki da gaggawa ba, to ilimin gaba da sakandire zai ci gaba da lalacewa kuma kimar ɗaliban Nijeriya za ta zube a idon duniya,” in ji Ministan.

Leave a Reply