Fursunoni 16 sun tsere daga Kurkukun Keffin jihar Nasarawa
Daga Shafaatu Dauda Kano
Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya (NCS) ta ce fursunoni 16 ne suka tsere daga gidan yari na Medium Security da ke Keffi, jihar Nasarawa, da safiyar ranar Talata.
Mai magana da yawun hukumar, Abubakar Umar, ya ce wasu fursunoni sun karya tsaron wurin, suka kai wa jami’an da ke bakin aiki hari, lamarin da ya haifar da tserewar su.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kai hari kurkukun Kuje
A kokarin shawo kan matsalar, jami’ai biyar sun ji raunuka daban-daban, inda biyu daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali suna karbar kulawar gaggawa kamar yadda wata majiya ta tattaro.









