Tsohon ministan noma Cif Audu Ogbeh ya rasu
Daga Jameel Lawan Yakasai
Iyalansa sun sanar da cewa tsohon ministan ya rasu a safiyar yau Asabar, yana da shekara 78 a duniya.
KU KUMA KARANTA: Shugaban hukumar zaɓen Bauchi Ahmed Makama ya rasu
Audu Ogbe ya riƙe mukamin minista a lokacin gwamnatin Muhammad Buhari, ya kuma riƙe shugabancin jam’iyyar PDP na ƙasa daga 2001 zuwa 2005.









