Shugaba Tinubu zai samar da layin dogo don rage cunkosun ababen hawa a Kano
Daga Jameel Lawan Yakasai
Gwamnatin Tarayya na shirin samar da titin jirgin ƙasa wanda zai riƙa zirga-zirga a cikin birnin Kano don rage cunkoson ababen hawa.
Hon. Abubakar Kabir Abubakar, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Kasafin Kuɗi ne ya bayyana haka inda ya ce aikin zai ci kimanin Naira tiriliyan ɗaya da rabi.
KU KUMA KARANTA: Najeriya ta karɓo rancen dala biliyan 1.3 don kammala layin dogon Kano zuwa Maraɗi
An shirya wannan aikin ne domin rage cunkoson ababen hawa da kuma samar da wadata ga tattalin arziƙi jihar da zarar an kammala shi.
Hon. Bichi ya kuma bayyana cewa akwai wasu ayyuka da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara a Arewacin Najeriya, waɗanda suka haɗa da gyaran ababen more rayuwa, kiwon lafiya, noma, ilimi, da tsaro.









