Shugaba Tinubu, har yanzu muna jira a bawa gwarazan gasa ‘yan Yobe nasu kyaututtukan

0
257
Shugaban Tinubu, har yanzu muna jira a bawa gwarazan gasa ‘yan Yobe nasu kyaututtukan
Hajiya Mairo Mudi

Shugaba Tinubu, har yanzu muna jira a bawa gwarazan gasa ‘yan Yobe nasu kyaututtukan

Daga Mairo Muhammad Mudi

A makon da ya gabata, Najeriya ta sake samun ƙaruwa daga ƙwallon ƙafa zuwa ƙwallon kwando har ma da fagen ilimi a ƙetare, ‘yan matan Nijeriya sun yi nasara a duniya. A ƙasar da galibi labaran marasa daɗi suka fi yawa, waɗannan nasarori uku sun zo a jere, suna tunatar da mu cewa in akwai dama da ƙarfafa gwiwa, ‘yan matanmu za su iya cin nasara a duniya.

Da farko, Super Falcons sun sake kafa tarihi ta hanyar lashe Kofin Mata na Afrika (WAFCON) na 2024 a ƙasar Morocco. Bayan haka, D’Tigress, ‘yan ƙwallon kwando mata na Najeriya, sun lashe Kofin AfroBasket na FIBA karo na biyar a jere, lallai abin alfahari ne sosai.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya baiwa ‘yan wasan Super Falcons kyautar lambar girma ta ƙasa da dala dubu 100 ga kowace ‘yar wasa

Shugaban ƙasa ya nuna farin cikinsa ga waɗannan nasarori ta hanyar ba su kyautar kuɗi har $100,000 kowacce ‘yar wasa, gidaje, da kuma kambun girmamawar na ƙasa watau OON. Wannan mataki ne da ya dace a kuma abin a jinjina masa.

Sai kuma wata nasara ta ban mamaki kuma mai inganci, wanda ake zanton wuta a maƙera kwatsam sai ga ta a masaƙa.
‘Yan mata guda uku daga Jihar Yobe ta Arewa Fatima Adamu, Falmata Bukar, da Aisha Usman sun wakilci Nijeriya a wani gasar turanci a London, inda suka doke ƙasashe 69 da suka shiga gasar daga faɗin duniya. Wannan ba ƙaramin abin alfahari ba ne. Daga yankin da galibi ake kiransa da masu koma baya a fannin ilimi ga talauci, wadannan ‘yan mata sun yin ba zanta game da lashe wannan gasar.

To sai dai, tambayar da ke ci wa mutane tuwo a ƙwarya ita ce:
Me yasa aka bi su da shiru da ko in kula?

Me ya sa aka yi wa Super Falcons da D’Tigress kyakkyawar kyauta, amma aka bar ‘yan matan Yobe da saƙon taya murna kawai daga fadar shugaban ƙasa? Ina kyautar girmamawa, ina kuɗi, ina gidaje, ina ɗaukaka da suma suka cancanta?

Bari na fito a mutum, wannan ba ƙoƙari ne na rage kimar waɗanda suka yi fice a fannin wasanni ba. Sun cancanci lambar yabo da su ka samu. Amma wannan yana kawo wasu wasi-wasi ga zukatan wasu, me ya sa muke girmama shahara watanni fiye da hazaƙa a ilimi?

KU KUMA KARANTA: Nafisa ta cancaci shugaba Tinubu ya yi mata kyautar dala dubu 100, gida da OON — Pantami

Tsawon shekaru, ana ba da muhimman kyaututtuka ga ‘yan wasa, mawaƙa, da shahararrun mutane, yayin da masu hazaka a fannin ilimi da fasaha ke kasancewa a gefe.

MTN Nigeria sun bayar da ₦150 miliyan ga Super Falcons, amma har yanzu babu ko kwatankwacin haka ga ‘yan matan Yobe. Ina MTN, Glo, Dangote, BUA da sauran manyan kamfanoni?

Ko saboda daga Yobe suka fito ne, yanki da ya sha fama da rikice-rikicen Boko Haram da koma baya? Ko saboda nasarar ba ta yi ɗaukin hankalin mutanen kudu ba ne a kafafen sada zumunta ba?

Abin da ya fi damun mutane shi ne, shugaban ƙasa ya san da nasarar domin ya tura saƙon taya su murna kawai. To, me ya hana ayi masu goma sha biyu ta arziki suma? Wannan ya ƙara cusa shakku a zukatan jama’ar Arewa: Shin, shugaban ƙasa ya fi damuwa da cigaban Kudu ne kawai?

Mutane da dama a Arewa sun fara ƙorafi game da yadda ake masu riƙon sakainar kashi bayan sun ba da goyon baya mai ƙarfi a zaɓen Shugaban ƙasa fiye da yankin da ya damu da su a yanzun. Kuma abin takaici shi ne, manyan jiga-jigan gwamnati daga Arewa sun yi shiru wata kila saboda kariyar kujerunsu. Amma wannan shiru yana haifar da rashin yarda da Shugaban ƙasa saboda haka ba taimakonsa suke ba.

A wannan gaba dole ne mu yabi Gwamnan Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, wanda bai jira fadar shugaban ƙasa ba. Ya karɓi ‘yan matan wanda aka tun farko shi ya ɗauki nauyinsu, ya kuma girmama su, ya nuna yana alfahari da su, ya kuma yi alƙawarin tallafa musu. Wannan shine irin shugabanci da ake buƙata.

Amma wannan nasara ba ta jihar Yobe ce kaɗai ba, nasara ce ta Nijeriya baki ɗaya.

KU KUMA KARANTA: ‘Yar jihar Yobe ta lashe gasar Turanci ta Duniya a Burtaniya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da damar gyara wannan kuskure ta hanyar ba wa wadannan ‘yan mata irin girmamawar da suka cancanta. Wannan zai isar da sako mai ƙarfi ga iyayen Arewa:
“’Ya’yanku mata suna da hazaƙar da Nijeriya ke alfahari da shi.
Wannan zai sa yara tururuwa zuwa makaranta.

Haka kuma, zai dawo da martabar ilimi a ƙasa da ke yawan ɗaukaka wasanni da shahara fiye da basira da ilimi.

Saboda haka, Shugaban Ƙasa, har yanzu muna jiran mataki mai akan ‘yan matan Yobe.

Fatima, Falmata, da Aisha sun yi wa Nijeriya hidima da za su alfahari. Yanzu kuma lokaci ne da Nijeriya itama ta sa su yi alfahari da ita.
mairommuhammad@gmail.com

Leave a Reply