Shugaba Tinubu ya taya gwaraza ‘yan jihar Yobe da suka lashe gasar turanci a Landan murna

0
154
Shugaba Tinubu ya taya gwaraza 'yan jihar Yobe da suka lashe gasar turanci a Landan murna

Shugaba Tinubu ya taya gwaraza ‘yan jihar Yobe da suka lashe gasar turanci a Landan murna

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya taya Nafisa Abdullahi Aminu, Ruƙayya Muhammad Fema, da Hadiza Kashim Kalli murnar nasarar lashe muhawara a gasar TeenEagle Global na shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan.

Nafisa mai shekaru 17, Ruƙayya mai shekara 15 da Hadiza su lashe kambun zinare duniya a fasahar Ingilishi.

Shugaba Tinubu ya yaba wa waɗannan haziƙan matasan bisa wannan bajinta, tare da tabbatar da cewa makomar al’ummar ƙasar na da kyau sosai ganin da yawa daga cikin matasanta sun zama zaƙaƙurai a fannin daban-daban na rayuwa.

KU KUMA KARANTA: Nafisa ta cancaci shugaba Tinubu ya yi mata kyautar dala dubu 100, gida da OON — Pantami

A cikin watan sanarwar da mai taimaka wa Shugaba Tinubu na musamman a fannin watsa labarai, Bayo Onanuga ya sa wa hannu, yi imanin cewa ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban ƙasa; “Don haka irin gagarumin jarin da gwamnatinsa ta yi a fannin da kuma kawar da matsalolin kuɗi ga ‘yan Nijeriya marasa galihu da ke neman manyan makarantu ta hanyar Asusun Bayar da Lamuni na Ilimi ta Nijeriya (NELFUND).

Tinubu ya jawo hankalin Nafisa, Ruƙayya, da Hadiza da su ci gaba da jajircewa wajen yin karatu tare da yi musu fatan alheri.

Sai dai tambayar da mutane ke yi ita ce, ko gwamnatin Tinubu za ta bai wa waɗannan haziƙan matasan irin kyautar da ya bai wa ‘yan ƙwallo mata na Nijeriya?

Leave a Reply