Na yi murabus ne domin maslahar al’ummar jihar Kano – Kwamishinan Sufuri

0
133
Na yi Murabis ne domin maslahar al'ummar jihar Kano - Kwamishinan Sufuri
Kwamishinan Sufuri na Kano Ibrahim Namadi

Na yi murabus ne domin maslahar al’ummar jihar Kano – Kwamishinan Sufuri

Daga Jameel Lawan Yakasai

Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi ya yi murabus daga mukaminsa sa’o’i kadan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karbi rahoton kwamitin bincike kan badakalar belin wani da ake zargi da sayar da miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.

Ana kallon wannan ci gaban a matsayin wani muhimmin mataki a ci gaba da jajircewar gwamnati wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, kwamishinan ya bayyana cewa ya yanke shawarar yin murabus ne saboda maslaha.

KU KUMA KARANTA: Kwamishinan Sufuri na Kano ya karɓi cin hancin Dala Dubu 30 kan karɓar belin dillalin miyagun ƙwayoyi

“A matsayina na memba na gwamnatin da ta kefafutukar yaki da safara da shaye-shayen miyagun kwayoyi, ya kamata in dauki wannan matakin.
.
“Yayin da nake ci gaba da kasancewa ba tare da wani laifi ba, ba zan iya yin watsi da nauyin tunanin jama’a da kuma bukatar kare nasarar da muka gina tare,” in ji shi.

Alhaji Namadi ya bayyana matukar godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya samu na yi wa jihar Kano hidima, tare da jaddada sadaukarwar sa ga tsarin shugabanci nagari.

KU KUMA KARANTA: Kwamishina a Kano Namadi, ya tsaya wa fitaccen dillalin miyagun ƙwayoyi Ɗanwawu a kotu

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din tare da yi wa tsohon kwamishinan fatan samun nasara a ayyukan sa na gaba. Ya kuma nanata matsayar gwamnatinsa na gaskiya a kan adalci, da’a, da yaki da laifukan da suka shafi muggan kwayoyi da munanan dabi’u da suka shafi matasa da sauran al’umma.

Leave a Reply