Gwamnatin Yobe za ta karrama gwarazan gasa ta duniya, Nafisa da Rukayya

0
212
Gwamnatin Yobe za ta karrama gwarazan gasa ta duniya, Nafisa da Rukayya

Gwamnatin Yobe za ta karrama gwarazan gasa ta duniya, Nafisa da Rukayya

Gwamnan jihar Yobe, Hon. (Dr) Mai Mala Buni, CON, COMN, ya amince da gudanar da wani biki na musamman don karrama Nafisa Abdallah mai shekara 17 da Rukayya Muhammad Fema mai shekara 15, bisa nasarar da suka samu na zama zakaru a gasar TeenEagle Global Finals 2025 da aka gudanar a birnin London, Kasar Ingila.

Nafisa da Rukayya, ‘yan asalin jihar Yobe ne, kuma dalibai ne a makarantar Nigerian Tulip International College inda suka wakilci Najeriya a gasar ta duniya, suka doke fiye da mutane 20,000 daga kasashe 69.

KU KUMA KARANTA: Nafisa ta cancaci shugaba Tinubu ya yi mata kyautar dala dubu 100, gida da OON — Pantami

Dukkan su biyun na daga cikin wadanda ke cin moriyar tsarin tallafin karatu na Gwamna Mai Mala Buni wanda ke daukar nauyin cikakken kudin makaranta ga dalibai 890 a Nigerian Tulip International College.

Gwamna Buni ya bayyana wannan gagarumar nasara a matsayin babban abin alfahari ga jihar Yobe da Najeriya baki daya.

Ya ce: “Wannan nasarar abin alfahari ce wadda ke kara karfafa dalilin da yasa muke zuba jari a fannin ilimi.”

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa harkar ilimi domin kowane yaro ya samu damar zuwa makaranta, tare da neman hadin gwiwar iyaye.

Ya kara da cewa: “Gwamnati ta sake gina makarantu da dama da ‘yan ta’adda suka lalata, ta samar da kayan daki, littattafai, kayan dakin gwaje-gwaje, tare da daukar malamai masu cancanta domin inganta ilimi a jihar — kuma har yanzu aiki yana kan tafiya.”

KU KUMA KARANTA: ‘Yar jihar Yobe ta lashe gasar Turanci ta Duniya a Burtaniya

A halin yanzu, akwai sama da dalibai 40,000 ‘yan asalin jihar Yobe da ke karatu a cikin gida da waje karkashin tsarin tallafin karatun gwamnati.

A baya-bayan nan, an gudanar da biki don murnar kammala karatun dalibai 167 da gwamnati ta dauki nauyinsu suka kammala karatu a fannonin likitanci, kimiyyar kwamfuta da injiniya a jami’o’in kasar India.

Mamman Mohammed Daraktan Yada Labarai na Ofishin Gwamna.

Leave a Reply