Gwamnan Yobe ya taya sabon Sarkin Gudi murna, ya yi kira ga sarakunan gargajiya da su kawo ƙarshen shan miyagun ƙwayoyi

0
301
Gwamnan Yobe ya taya sabon Sarkin Gudi murna, ya kira ga sarakunan gargajiya da su kawo ƙarshen shan miyagun ƙwayoyi 
Gwamna Buni tare da Sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Gadaka

Gwamnan Yobe ya taya sabon Sarkin Gudi murna, ya yi kira ga sarakunan gargajiya da su kawo ƙarshen shan miyagun ƙwayoyi

Gwamnan Yobe ya taya sabon Sarkin Gudi murna, ya buƙaci sarakunan gargajiya da su magance matsalar shan miyagun ƙwayoyi

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Dakta Mai Mala Buni, CON, ya taya sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed murna, inda ya bayyana naɗa shi Sarki ɗin, a matsayin wani mataki da jama’a suka amince da shi.

Gwamnan ya miƙa saƙon taya murnar sa yayin ziyarar godiya da tawagar Masarautar Gudi suka kai gidan gwamnati dake Damaturu ranar litinin.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya halarci jana’izar Sarkin Gudi a garin Gadaka

“Ka kasance ɗan siyasa mai nasara kuma yanzu ka zama sarkin gargajiya, babu wanda ya isa ya faɗa maka darajar haƙuri da zama da mutane, ka ƙware sosai, a wannan fanni” inji Gwamna Buni.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya ba Alhaji Ismaila Ahmed lafiya, ya kuma yi addu’a ga marigayi Sarki Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Kaji, inda ya roƙi Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya saka masa da Aljannar Firdausi.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya naɗa Ismaila Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi

Gwamna Buni ya yi amfani da wannan dama wajen yin ƙira ga masu riƙe da sarautun gargajiya a faɗin jihar da su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, wanda ya bayyana a matsayin wata barazana da ke ƙara ƙamari musamman a Arewacin Najeriya.

“A matsayin masu kula da al’ada da al’adu, sarakunan gargajiya suna da muhimmiyar rawa wajen tsara kyawawan ɗabi’un matasanmu,” in ji shi. “Ba kamar shugabannin siyasa waɗanda ke yin wa’adi ba, sarakunan gargajiya sune shugabanni na rayuwa tare da tasiri mai ɗorewa.

Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da cibiyoyin gargajiya domin yaƙar ƙaruwar shan miyagun ƙwayoyi.

“Masarautun gargajiya sune mafi girman ababen girmamawa da mutuntawa a cikin al’umma, tare da tasiri mai mahimmanci. Tare da ƙoƙarin gwamnati, za ta iya zama wani ƙarfi a kan barazanar miyagun ƙwayoyi,” in ji Gwamnan.

 

 

 

Leave a Reply