Gwamnan Kano ya umarci KAROTA, FRSC da su tilasta wa masu ababen hawa bin dokokin hanya
Daga Jameel Lawan Yakasai
Gwamnatin Kano tace duk da kokarin da tayi na sanya fitilun haska Titi da fitilun bada hannu, wasu direbobi da mazauna birnin Kano na ci gaba da karya dokokin hanya, watsi da matakan tsaro, da kin girmama sabbin kayayyakin da aka saka musamman fitilun tituna.
Saboda haka, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci Hukumar Kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar Kano (KAROTA) tare da Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) da su gaggauta kaddamar da cikakken aikin tilasta bin dokokin hanya, musamman bin dokar fitilar bada hannu ta titi a cikin birnin.
KU KUMA KARANTA: Shugaban hukumar KAROTA a Kano, ya buƙaci ma’aikatansa su ninka ƙoƙarin da suke yi don ƙara samar wa hukumar kuɗin shiga
Gwamnati ta kara jaddada cewa, motoci na gaggawa kawai irin su na kashe gobara, motocin daukar marasa lafiya da na hukumomin tsaro da ke bakin aiki ne kadai aka amince su karya doka idan suna cikin aikinsu na gaggawa kamar yadda dokar Kasa ta bada dama.
Gwamnati ta gargadi cewa daga yanzu duk wani mutum ko kungiya da aka kama suna kokarin kawo cikas ga wannan yunkuri na gyaran birni ko kuma karya dokokin hanya, za su fuskanci fushin doka.
Haka zalika, an gargadi duk wani jami’in gwamnati da ya shiga cikin harkar dakatar da jami’an kula da zirga-zirgar ababen hawa domin kare wanda ya karya doka, za a kai rahotonsa ga hukumar da ta dace domin hakan na nuni da yunkurin bata suna ko hana nasarar wannan gwamnati.









