Ba abin da nafi tsoro a rayuwa irin talauci – Jaruma Jemima Osunde

0
148
Ba abin da nafi tsoro a rayuwa irin talauci - Jaruma Jemima Osunde
Jaruma Jemima Osunde

Ba abin da nafi tsoro a rayuwa irin talauci – Jaruma Jemima Osunde

Daga Jameel Lawan Yakasai

Jarumar fina-finai, Jemima Osunde, ta bayyana cewa talauci ne mafi girman tsoro a rayuwarta, tana mai cewa ba za ta iya rayuwa da shi ko kadan ba.

Ta bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da ita a shirin The Culture League Podcast da dan wasan Super Eagles, Victor Boniface, ke gabatarwa.

KU KUMA KARANTA: Hukumar tace fina-finai a Kano ta dakatar da jaruma Samha M Inuwa

Osunde ta ce tana da karfin hali wajen jure yawancin kalubale na rayuwa, amma talauci abu ne da ba ta da ikon jurewa. Ta kuma jaddada cewa tana daraja mutuncinta da tarbiyyarta fiye da komai, kuma za ta yi duk mai yiwuwa don guje wa talauci, matuƙar hakan bai tauye kimarta ba.

“Ba na so na ma dandana talauci. Ina jin dadin inda nake yanzu, kuma bana son komawa baya,” a cewar ta.

Leave a Reply