Babu kalmar ‘Inconclusive’ a tsarin dokokin zaɓen Najeriya – INEC

0
289
Babu kalmar "Inconclusive" a tsarin dokokin zaɓen Najeriya - INEC

Babu kalmar ‘Inconclusive’ a tsarin dokokin zaɓen Najeriya – INEC

Daga Jameel Lawan Yakasai

Kwamishinan Zaɓe na Hukumar INEC a jihar Kano, Malam Abdu Zango ne ya bayyana hakan, yayin wani taron wayar da kai da hukumar zaɓen ta shirya da masu ruwa da tsaki a Kano, a ranar Alhamis, gabannin zaɓen cike gurbi da na wasu mazaɓu da za a maimaita a ranar 16 ga watan Agusta.

KU KUMA KARANTA: INEC ta sanya ranar 16 ga Agusta don zaɓen cike gurbi a mazabu 16

Ya ce, wannan kalma ba ta da wata madogara a doka, duk da cewa a baya ana yawan amfani da ita lokacin da adadin ƙuri’un da aka soke ya fi yawan tazarar ƙuri’un da ke tsakanin ‘yan takara.

Leave a Reply