Ƙungiyar likitocin dabbobi ta Najeriya ta yaye sabbin ɗalibai 38 a jami’ar Ahmadu Bello

0
235
Ƙungiyar likitocin dabbobi ta Najeriya ta yaye sabbin ɗalibai 38 a jami'ar Ahmadu Bello
Sabbin ɗaliban dabbobi da aka yaye a jami'ar Ahmadu Bello

Ƙungiyar likitocin dabbobi ta Najeriya ta yaye sabbin ɗalibai 38 a jami’ar Ahmadu Bello

Daga Idris Umar, Zariya

Ƙungiyar Likitocin Dabbobi ta Najeriya (VCN) ta sabbin ɗalibai 38 da suka kammala karatu daga Sashen Kiwon Lafiyar Dabbobi na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya. An gudanar da bikin ne a ranar Juma’a, 1 ga Agusta, 2025 a Cibiyar CBN da ke harabar jami’ar, a Samaru.

A yayin bikin, Mataimakin Shugaban Jami’ar (na Harkokin Gudanarwa), Farfesa Ahmed Doko Ibrahim, wanda ya wakilci Shugaban Jami’ar, Farfesa Adamu Ahmed, ya taya sabbin likitocin dabbobi murna bisa nasarar da suka cimma bayan shekaru na karatu da jajircewa. Ya yaba wa Sashen Kiwon Lafiyar Dabbobi bisa gudunmawar da yake bayarwa ga ci gaban jami’ar, tare da bukatar sabbin likitocin da su rike gaskiya da kwarewa a aikinsu, su kuma rika tunawa da makarantar da ta rainesu.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta yaba wa Gwamnatin Zamfara kan ƙarin Albashin Likitoci

Shugaban Sashen, Farfesa Junaidu Kabir, ya nuna godiyarsa ga shugabancin jami’ar da kuma shugaban Hukumar Likitocin Dabbobi, Farfesa Sheikh Mathew Adamu, da Sakatare, Dakta Oladotun E. Fadipe, bisa goyon bayan da suka ba sashen a lokacin shugabancinsa. Ya kuma yabawa sabbin likitocin da iyayensu bisa sadaukarwa da jajircewa da suka yi har suka kai ga wannan nasara.

Bakun da aka gayyata domin jawabi a taron shi ne Dakta Samuel Ankali, tsohon mai ba marigayi Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan al’amuran nakasassu. Ya bukaci sabbin likitocin da su dage wajen neman ci gaba, su kuma shiga fannoni daban-daban domin samun wakilcin likitocin dabbobi a kowane mataki na shugabanci.

Dakta Oladotun Fadipe ne ya rantsar da sabbin likitocin domin kaddamar da su a hukumance cikin sana’ar.

An karrama wasu baki da suka halarci bikin tare da bayar da kyaututtuka ga daliban da suka fi kowa kwarewa a fannin karatu: Dakta Hamza Isa, wanda ya samu CGPA 4.18, da Dakta Rofiat Omotayo Olafimihan, mai CGPA 4.04.
Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Leave a Reply