Bayern Munchen ta sayi Luis Diaz daga Liverpool

0
122
Bayern Munchen ta sayi Luis Diaz daga Liverpool
Luiz Diaz

Bayern Munchen ta sayi Luis Diaz daga Liverpool

Daga Jameel Lawan Yakasai

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munchen ta sayi dan wasan gaban Liverpool, Luis Diaz akan kuɗi da zai ƙaru har zuwa Dala miliyan 86.5.

Diaz, Dan ƙasar Colombia, ya rattaba hannu a Bayern ta ƙasar Jamus akan kwantar shi ta shekaru 4, har zuwa 2029 kenan.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar Liverpool ta samu tazarar maki 8 akan teburin gasar Firimiya

Da wannan siyayya, Diaz ya zama shine dan wasa na uku mafi tsada a tarihin Bayern.

Leave a Reply