Allah Ya yiwa mai martaba Sarkin Gudi Alhaji Isah Bunowo rasuwa
A yau Alhamis ne fadar mai martaba Sarkin Gudi dake jihar Yobe ta sanar da rasuwar Sarkin na Gudi Alhaji Isah Bunowo Ibn Madubu Khaji.
Za a yi jana’izarsa gobe juma’a da misalin ƙarfe 2:00 na rana a fadarsa da ke Gadaka a ƙaramar hukumar Fika da ke jihar Yobe.
KU KUMA KARANTA: Sarkin Tikau na jihar Yobe ya rasu
Haka ma, Fadar mai martaba Sarkin Fika ta sanar da rasuwar na Sarkin Gudi.
Cikakken rahoto zai zo daga baya.









