‘Yansanda a Kano sun cafke riƙaƙƙen ɗan daba Mu’azu Barga 

0
344
'Yansanda a Kano sun cafke riƙaƙƙen ɗan daba Mu'azu Barga 

‘Yansanda a Kano sun cafke riƙaƙƙen ɗan daba Mu’azu Barga

Daga Jameel Lawan Yakasai

Rundunar ’Yansandan Kano ta cafke wani riƙaƙƙen ɗan daba da ake nema ruwa a jallo, mai suna Mu’azu Barga, bisa zargin aikata fashi da makami da haddasa rikice-rikicen Daba a unguwar Sheka.

Wannan na cikin wani saƙo da Kakakin Rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da hakan.

KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda a Kano sun kama wani ƙasurgumin ɗan daban da ake nema ruwa a jallo

Ya ce jami’an sashin yaki da Daba na rundunar ne suka kama Barga bayan dogon bincike da kuma koke-koke daga al’umma game da laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Leave a Reply