Tinubu ya yaba wa Super Falcons bisa lashe kofin gasar WAFCON karo na 10

0
209
Tinubu ya yaba wa Super Falcons bisa lashe kofin gasar WAFCON karo na 10
Super Falcons suna murnar lashe kofin WAFCON

Tinubu ya yaba wa Super Falcons bisa lashe kofin gasar WAFCON karo na 10

Daga Jameel Lawan Yakasai

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tawogar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, murnar lashe kofin Gasar Ƙwallon Ƙafa ta Nahiyar Afirka ta Mata (WAFCON) na shekarar 2024, inda su ka lashe gasar karo na 10 a tarihi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa Najeriya ta farke kwallaye 2 da aka fara zura mara a raga, inda ta doke kasar Morocco mai masaukin baki 3-2 a wasan karshe da aka fafata a Rabat, Morocco.

KU KUMA KARANTA: Najeriya ta ci kyautuka 3 a bikin ba da lambobin yabo na ƙwallon ƙafa a Afirka

Kakakin Shugaban Kasa, Mista Bayo Onanuga ne ya isar da sakon Shugaban kasar jim kadan bayan wasan a jiya Asabar.

Tinubu ya yaba wa nasarar a matsayin alamar juriya da kuma alfaharin kasa.

Leave a Reply