No menu items!

Sample Page Title

Date:

Sarkin Gusau, Ibrahim Bello ya rasu yana da shekaru 71

Daga Jameel Lawan Yakasai

Sarkin Gusau, Dakta Ibrahim Bello, ya rasu a jiya Alhamis a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya.

Sakataren Majalisar Masarautar ne Alhaji Sambo A. Sambo ne ya bayyana hakan, inda ya ce sarkin ya rasu yana da shekaru 71 a duniya.

An nada Dr. Ibrahim Bello a matsayin sarki a ranar 16 ga Maris, 2015, a zamanin tsohon Gwamna, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar.

Marigayin shi ne Sarkin Gusau na 15, kuma jinin Shehu Usman Ɗan Fodiyo ne.

Marigayin ya bar mata da ‘ya’ya da jikoki da dama. Ya kasance ƙwararren ma’aikacin jinya (nurse) wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa fannin kiwon lafiya a jihohin Sokoto da Zamfara.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...