An kama mai yin tsire da naman Kare a Kano
Daga Shafaatu Dauda Kano
Gungun Wasu matasa sun yi nasarar gano wani mutum mai sayar da tsiren naman Kare ga Mutane a Kano.
Matasan sun kama shi ne a bayan katangar Audu Baƙo Sakateriya dake jihar Kano.
Sun kama shi ne da wuƙa da tsinkayen yin tsiren. Zuwa yanzu dai an miƙa shi ga hukumar ‘yansanda.
KU KUMA KARANTA: Yadda amarya ta kashe kishiyarta akan tsire
Kafin haɗa wannan ratohon wakiliyar Neptune Prime ta tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa amma bai ɗauki wayar ba.









