Gwamnan Katsina ya tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Daura zuwa Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi wani ɗan karamin hatsarin mota a yammacin ranar 20 ga watan Yuli, 2025, a lokacin da yake tafiya kan hanyar Daura zuwa Katsina a wani ɓangare na gudanar da aikinsa.
A cewar wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na Gwamnan ya fitar, Ibrahim Kaula Mohammed, gwamnan bai samu munanan raunuka ba kuma yana cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali.
KU KUMA KARANTA: Za a gina birnin Dawakai ma fi girma na farko a Katsina
Sanarwar ta ƙara da cewa Gwamna Radda ya ci gaba da kasancewa cikin farin ciki kuma ya nuna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya ba shi kariya. Ya kuma miƙa godiyarsa ga al’ummar jihar Katsina da duk waɗanda suka yi addu’o’i da kuma nuna damuwarsu.
Lamarin dai bai yi muni ba, kuma ana sa ran Gwamnan zai ci gaba da gudanar da ayyukan sa.









