Gwamnan Kaduna ya ba da umarnin a saki Fatima Zahra, fitacciyar ‘yar Tiktok da aka kama
Biyo bayan tir da Allah wadai da jama’a suka yi, an tabbatar cewa Fatima Zahra Saidu, Tiktoker daga Zaria da jami’an ‘yansanda suka kama ranar Juma’a saboda sukar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, an umurci a sake ta nan take. Suna tuhumar ta ne da murna da mutuwar Buhari.
Gwamnan Jihar Kaduna ya tabbatar da cewa ya bayar da umarni ga rundunar ‘yansanda a Zariya da su saki Fatima Zahra nan take.
KU KUMA KARANTA: Kotu a Kano ta yankewa wasu ‘yan Tiktok 2 ɗaurin shekara 1 a gidan gyaran hali
Wannan ci gaba ne da kuma babbar nasara ga ‘yancin faɗin albarkacin baki, da kuma shaida cewa muryar jama’a tana da ƙarfi. Amma hakan ma na tuna mana cewa ‘yanci yana buƙatar tsayawa tsayin daka wajen kare shi.









