KAROTA ta haramtawa manyan motoci hawa gadojin sama a Kano

0
232
KAROTA ta haramtawa manyan motoci hawa gadojin sama a Kano

KAROTA ta haramtawa manyan motoci hawa gadojin sama a Kano

Daga Shafaatu Dauda Kano

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta sanar da haramta hawa gadojin sama da ke birnin Kano ga manyan motocin ɗaukar kaya, tare da fara cafke masu karya wannan doka.

Mataimakin Shugaban hukumar, Auwal Lawan Aranposu ne ya bayyana hakan a hirarsa da Arewa Updates a ranar Litinin, 14 ga Yuli, 2025.

Aranposu ya bayyana cewa tuni hukumar ta kama wasu daga cikin manyan motocin da suka karya doka ta hanyar hawa gadar sama, kuma suna hannun KAROTA domin ɗaukar matakin da ya dace.Ya ce, “Mun fara cafke motocin da suka karya doka, kuma za mu ci gaba da sanya ido domin ganin an bi wannan ƙa’ida da aka shimfiɗa. Doka za ta yi aiki ga duk wanda aka samu da laifi.”

KU KUMA KARANTA: Hukumar KAROTA a Kano ta gargaɗi masu kai wa jami’anta farmaki

Ya kuma ja kunnen direbobi da masu manyan motoci da su guji hawa gadojin sama a fadin Kano, yana mai cewa wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da tsaro da kyakkyawan tsari a harkar zirga-zirga a fadin Jihar.

A cewar KAROTA, gadojin sama a Kano an gina su ne domin amfanin kananan motoci da masu tafiya a ƙasa, ba don manyan motocin ɗaukar kaya ba.

Leave a Reply