Kano Pillars ta yi yarjejeniyar talla da ‘RFI Hausa’ a rigunan wasansu

0
257
Kano Pillars ta yi yarjejeniyar talla da 'RFI Hausa' a rigunan wasansu

Kano Pillars ta yi yarjejeniyar talla da ‘RFI Hausa’ a rigunan wasansu

Daga Jameel Lawan Yakasai

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Najeriya, tana farin cikin sanar da wata babbar yarjejeniyar haɗin gwiwa ta talla tare da Radio France Internationale (RFI) Hausa, fitaccen gidan Rediyon watsa labarai na duniya da ke ba da gudummawa ga wasanni, al’adu, da haɗa al’umma a cikin Najeriya da sauran ƙasashe.

A ƙarƙashin wannan sabuwar yarjejeniyar tallafawa, RFI Hausa ta zama babban mai tallafawa Kano Pillars FC a kakar wasa mai zuwa, Za a ga tambarin RFI Hausa a gaban rigunan gida dana waje, na ƙungiyar Kano Pillars, da kuma a duk wani kayan talla na hukuma.

Wannan haɗin gwiwar ya ƙunshi dukkan ƙungiyoyin Kano Pillars, ciki har da ƙungiyar B, ƙungiyoyin matasa (U19, U15, U13), da sauransu.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta naɗa Ahmed Musa a matsayin manajan Darakta na Kano Pillars

Wannan sabuwar haɗin gwiwa, wanda ke ƙarƙashin jagorancin sabon Manaja Janar kuma tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Najeriya Ahmed Musa, zai taimaka wajen ɗaukar Kano Pillars zuwa mataki mafi girma. RFI Hausa za ta ba da babban tallafi, ciki har da:

• Cikakken tallafin sabbin riguna ga dukkan ƙungiyoyin
• Kayan aikin watsa labarai na zamani ga kulob din
• Horar da ƙungiyar yada labarai ta Kano Pillars kan ƙirar bidiyo na ƙwararru
• Cikakken dabarun sadarwa
• Haɗin gwiwar watsa labarai tare da bugawa a dandamalin RFI Hausa

“Wannan wani sabon fari ne ga Kano Pillars FC yayin da muke ƙoƙarin ɗaukaka wannan babbar ƙungiya zuwa matsayi mai girma, A matsayina na Manajan Janar, ina so in tabbatar wa magoya baya, masu ruwa da tsaki, da kuma dukkan al’ummar ƙwallon ƙafa cewa kofofinmu a koyaushe a buɗe suke, Muna da azama kan gaskiya, ci gaba, da kyakkyawan aiki, kuma na yi imani cewa kyakkyawan lokaci mai cike da nasara da ɗaukaka yana jiran Sai Masu Gida.” Inji Ahmed Musa, Manajan Janar, Kano Pillars FC.

“RFI Hausa tana alfaharin yin haɗin gwiwa da irin wannan muhimmiyar ƙungiyar ƙwallon ƙafa da mutane ke ƙauna, Mun yi imani da hangen nesa da makomar ƙungiyar, kuma za mu taimaka wajen tura ta gaba sosai.” Inji Joe Penney, Darakta, France Médias Monde Nigeria.

Wannan haɗin gwiwa yana nuna kwazo kan kyakkyawan aiki a filin wasa da kuma ba da labarai masu ƙarfi a wajen sa, Dukkan Kano Pillars FC da RFI Hausa suna sa ran wata kakar wasa mai cike da nasara da kuma haɗa kai tare da magoya baya.

Leave a Reply