Hauhawar farashin kaya ya sauƙa zuwa kashi 22.22% a watan Yuni — NBS

0
386
Hauhawar farashin kaya ya sauƙa zuwa kashi 22.22% a watan Yuni — NBS

Hauhawar farashin kaya ya sauƙa zuwa kashi 22.22% a watan Yuni — NBS

Daga Shafaatu Dauda Kano

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kaya a Najeriya ya ragu zuwa kashi 22.22 cikin dari a watan Yuni 2025, daga kashi 22.97% da aka samu a watan Mayu.

Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton “Hauhawar Farashi” (Inflation Report) da rahoton “Consumer Price Index” (CPI) da hukumar ta fitar a Abuja, wanda ke nuna ci gaban da aka samu a fannin tattalin arzikin ƙasar.
A cewar rahoton, a bangaren hauhawar farashin abinci, an samu raguwa mai yawa daga kashi 40.87% a watan Yuni na shekarar 2024, zuwa kashi 21.97% a Yuni 2025 — wanda ya nuna raguwar kashi 18.90 cikin dari

Rahoton ya bayyana cewa Jihar Zamfara ce ta fi saukin hauhawar farashi da kashi 9.90%, sai Yobe da kashi 13.51%, da kuma Sokoto da kashi 15.78%.

KU KUMA KARANTA: Tattalin arziƙin Najeriya ya bunƙasa da kaso 3.84 cikin 100 a zango na 4 na 2024 – NBS

Adeniran ya ƙara da cewa, “Sabunta tsarin ya haɗa da ƙara wasu kayayyakin bukatu da kuma sabbin hanyoyin tattara bayanai domin samar da cikakken hoto na yadda tattalin arziki ke tafiya.”

Babban Jami’in Ƙididdiga na Ƙasa, Adeyemi Adeniran, ya ce sabunta tsarin da ake amfani da shi wajen ƙididdige CPI daga ma’aunin shekarar 2009 zuwa na 2024, ya taimaka matuƙa wajen dacewa da halin da tattalin arzikin ƙasa ke ciki a halin yanzu.

Leave a Reply