An ɗauko gawar Buhari daga Landan zuwa Najeriya
Gawar tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta baro birnin London, Birtaniya, da safiyar Yau Talata, zuwa garin Daura a Jihar Katsina, domin gudanar da jana’izar sa.
Jaridar PUNCH Online ta ruwaito cewa an dauko gawar tsohon shugaban kasar ne a jirgin saman Najeriya.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ke jagorantar tawagar gwamnatin tarayya da shirye-shiryen dawo da gawar tsohon shugaban kasar zuwa gida.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Yobe ta ayyana gobe Talata a matsayin ranar hutu, don juyayin mutuwar Buhari
A jiya Litinin, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai karɓi gawar tsohon shugaban kasar a Katsina kafin a kai ta Daura don binne wa.
Ministan Watsa Labarai da Tsare-Tsaren Ƙasa, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Abuja.









