Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rasu a Landan
Daga Shafaatu Dauda Kano
Rahotanni sun nuna cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu a birnin London bayan fama da rashin lafiya
Rasuwar tasa ta faru ne yau, inda tsohon hadiminsa, Bashir Ahmad ya tabbatar da hakan ciki Damuwa da alhini
Ana sa ran nan gaba kadan za a sanar da lokacin masa janaiza da dawo da gawar shi nan Najeriya daga London
Tsohon shugaban kasa na Najeriya, Muhammadu Buhari, ya rasu a yau Asabar, 13 ga Yuli, 2025 a birnin London na ƙasar Ingila.
Labarin rasuwar tasa ya girgiza al’ummar Najeriya da ma kasashen duniya, inda fadar shugaban kasa ta tabbatar da faruwar lamarin bayan makonni na rade-radin rashin lafiyarsa.
Buhari, wanda ya shugabanci Najeriya daga 2015 zuwa 2023, ya shafe kwanaki da dama yana jinya a wani asibiti da ba a bayyana ba a London kafin rasuwar tasa.









