Za mu ci gaba da wasu ayyukan da Buhari ya fara – Tinubu
Daga Idris Umar, Zariya
Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kudirin gwamnatinsa na ci gaba da ƙarfafa manufofin gyare-gyaren da gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta assasa, domin tabbatar da ci gaba da isar da amfanin dimokuraɗiyya ga al’umma baki ɗaya.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin bikin ƙaddamar da wani littafi mai take “According to the President: Lessons from a Presidential Spokesman’s Experience” wanda tsohon Mai Magana da yawun Shugaban Ƙasa Buhari, Malam Garba Shehu ya rubuta. An gudanar da taron ne a birnin tarayya Abuja a ranar Talata.
Shugaban Ƙasar, wanda aka wakilta ta hannun Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya ce tsarin “Sabon Fata” na gwamnatinsa ya ginu ne bisa ginshiƙan da gwamnatin Buhari ta kafa.
“Kokarin wata gwamnati shi ne tushen nasarar ta gaba,” in ji Shugaba Tinubu. “A wannan fanni, ina yaba da ƙoƙarin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, kuma ina tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa wannan gwamnati za ta ci gaba da ƙarfafa gyare-gyaren da aka fara a wancan lokaci.”
KU KUMA KARANTA: Ba zan taɓa juyawa APC baya ba – Buhari
Shugaba Tinubu ya bayyana littafin a matsayin muhimmiyar ma’ajiyar ilimi ga ‘yan jarida, masu tsara manufofi, masana tarihi, da al’umma gaba ɗaya. Ya kuma jinjinawa tsohon shugaban ƙasa Buhari kan shugabancin da ya ginu kan gaskiya, rikon amana, kyakkyawan tanadi, da ƙaunar ƙasa.
A nasa jawabin, tsohon Shugaban Ƙasa Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya yabawa Buhari saboda jajircewarsa da gaskiya wajen fuskantar ƙalubale da dama da suka haɗa da matsalar tsaro, yana mai jinjina wa Sojojin Najeriya bisa sadaukarwarsu wajen kare ƙasar.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana tarihin rayuwar Malam Garba Shehu daga aikin jarida har zuwa matsayin mai magana da yawun shugaban ƙasa, yana mai cewa ya taka rawar gani da kwarewa wajen gudanar da ayyukansa cikin kwarewa da dabara.
Shi ma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce nasarar da Garba Shehu ya samu daga matsayin mai magana da yawun kamfen zuwa na fadar shugaban ƙasa ta samo asali ne daga cancanta da gwanintarsa a fagen watsa labarai. Ya ƙara da cewa littafin, wanda aka raba kashi uku—Gabatarwa, Gado na Shugabancin Sauyi, da Gado na Buhari daga 2015 zuwa 2023—na ɗauke da muhimman darussa game da rayuwa da salon mulkin Buhari.
Taron ya tattaro manyan baki daga fannoni daban-daban na gwamnati da jama’a, inda aka nuna girmamawa ga tsohon shugaban ƙasa Buhari da tsohon mai magana da yawunsa, Garba Shehu.
Anyi masu ruwan addu’o’i yayin kammala taron.









