Tsohon ɗan wasan Najeriya, Peter Rufai ya rasu

0
367
Tsohon ɗan wasan Najeriya, Peter Rufai ya rasu
Marigayi Peter Rufai

Tsohon ɗan wasan Najeriya, Peter Rufai ya rasu

Daga Jameel Lawan Yakasai 

Tsohon mai tsaron ragar Super Eagles ta Nijeriya, Peter Rufai, ya riga mu gidan gaskiya bayan shafe shekaru 61 a doron kasa.

Super Eagles ce ta bayyana rasuwar golan cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na X a wannan Alhamis din.

KU KUMA KARANTA: Najeriya ta ci kyautuka 3 a bikin ba da lambobin yabo na ƙwallon ƙafa a Afirka

Fitaccen golan wanda yana cikin tawagar Super Eagles da ta lashe Kofin Nahiyyar Afirka na AFCON a shekarar 1994 ya rasu ne bayan fama da jinya.

Marigayi Peter Rufai wanda ake yi wa inkiyar Dodo Mayana, ya buga wa kungiyar Farense ta Kasar Portugal kusan wasanni 60.

A lokacin rayuwarsa, Peter Rufai ya mallaki makarantar koyon kwallon kafa da ake kira ‘Dodo Mayana’ a Jihar Legas, inda ake zakulo yara daga fadin Nijeriya a taimaka musu.

Peter Rufai ya yi makarantu da dama, yana kuma da takardu da shaidar karin ilmi na Diploma tare da Hukumar Kwallon Kafar Turai ta UEFA.

Tsohon golan ya karanci abubuwan da su ka shafi ladubba da kuma horaswa. Sannan ya yi kwas-kwasai da dama da Hukumar UEFA.

Peter Rufai yana da digiri na biyu) a fannin Harkar kasuwanci.

Leave a Reply