Jami’ar Bayero ta Kano ta zaɓi Farfesa Haruna Musa Ɗambatta a matsayin sabon shugaba 

0
690
Jami'ar Bayero ta Kano ta zaɓi Farfesa Haruna Musa Ɗambatta a matsayin sabon shugaba 
Jami'ar Bayero ta Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), ta zaɓi Farfesa Haruna Musa a matsayin sabon shugaban jami’ar (Vice Chancellor).

Musa ya zama shugaban ne bayan jami’ar ta gudanar da zaɓe tsakanin ƴan takarar kujerar a yau Talata a harabar jami’ar.

Farfesa Haruna Musa Ɗambatta

KU KUMA KARANTA: An kama malaman bogi a jami’ar Bayero da ke Kano

Ga jerin yadda sakamakon zaɓen ya kasance:

1. Farfesa Haruna Musa = 853

2. Farfesa Mahmoud Umar Sani = 367

3. Farfesa Muhammad Sani Gumel = 364

4. Farfesa Adamu Idris Tanko = 161

5. Farfesa Bashir Muhammad Fagge = 18

Leave a Reply