Ana Zargin wani magidanci da kashe ‘yarsa Sakamakon Dukanta da Itace a kano
Daga Shafaatu Dauda Kano
Al’ummar unguwar Dawakin Dakta, da ke jihar Kano, sun shiga alhini bisa yadda aka zargi wani mutum da sanadiyyar rasuwar Ƴar sa budurwa mai suna Zainab a unguwar, sakamakon dukan ta da Itace.
Tunda fari dai mutumin mai suna Adamu Muhammad, ya yi zargin cewa ƴar tasa tana zaman kan ta a wasu wurare, lamarin da ya ke ci masa Tuwo a Ƙwarya, har yake tsawatar mata don ganin ta dai na.
Da yake ganawa da manema labarai, yayan budurwar, mai suna Yahaya Adamu Muhammad, ya ce bayan da Zainab ta fita yawon zaman kan nata ne a baya-bayan nan, ran mahaifin su ya ɓaci, da ta dawo gida kuma, aka yi zargin mahaifin nasu ya ɗaure ta tare da kulle ta,
Yaci gaba da cewa, daga nan ne mahaifin nasu ya kuma yi wa ƙanwar tasa dukan Kawo Wuƙa da wani Itace a ranar Litinin, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar ta a safiyar Talata 17 ga watan Yunin 2025.
Shima wani shaidar gani da ido mazaunin unguwar mai suna Muhammad Muttaƙa Eto Dawakin Dakata, ya shaidawa Manema labarai, cewar sun shiga cikin tashin hankali a yanayin da suka ga marigayiya Zainab, ɗaure da wata Sarƙa, bayan da aka yi zargin mahaifin nata ya yi mata dukan har ta riga mu gidan gaskiya.
READ ALSO:Gwamnatin Tarayya zata haɗa hannu da Gwamnatin Jihar Kano domin gina cibiyar kasuwanci ta zamani
Malama Mai Jidda, ita ce mahaifiyar marigayiya Zainab Adamu, ta ce bayan da mijin nata ya ɗaure ƴar tasu sannan ya yi mata dukan, ko da ta bukaci ya kwance ta amma ya gaza yin hakan, sai wani ta kira ya kwance ta a daren Litinin, inda da safiyar Talata ta bata Ruwa domin ta sha sai dai bai tafi ba, bayan ta kwantar da ita ne kuma ta rasu da ƙarfe 06:00 na safiyar Talata.
yake nasa jawabin akan lamarin, kwamandan tsaro na unguwar Dawakin Dakata, Munzali Aliyu Umar, ya ce bayan da marigayiya Zainab Adamu, ta rasu ne aka sanar musu faruwar lamarin, inda suka halarci gidan tare da sanar da Baturen Ƴan Sanda na Dawakin Dakata, CSP Awaisu, bayan da ya turo jami’an su suka kai marigayiyar Asibiti, tare da yin gaba da mutumin da ake zargin.
Akan lamarin wakiliyar Neptune prime ta yi ƙoƙarin ji daga ɓangaren mai magana da yawun rundunar Ƴan Sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta wayar salula, sai dai haƙan ta bata cimma ruwa ba.
Allah ya kyauta









