‘Yan Yahoo na kunyata Najeriya a idon duniya — shugaban EFCC

0
202
'Yan Yahoo na kunyata Nijeriya a idon duniya — shugaban EFCC

‘Yan Yahoo na kunyata Najeriya a idon duniya — shugaban EFCC

Daga Jameel Lawan Yakasai

Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa masu damfara ta yanar gizo da aka fi sani da ‘yan yahoo-yahoo suna jawo wa Najeriya abin kunya a idon duniya.

Olukoyede ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da ya gudanar a ranar Litinin a hedikwatar hukumar da ke Abuja.

A cewarsa, ‘yan yahoo-yahoo sun jefa kowanne ɗan Najeriya cikin halin zargi da rashin gaskiya a idanun jami’an shige da fice a ƙasashen waje.

KU KUMA KARANTA:‘Yanbindiga sun kashe mutane 2, sun sace mutum 1 a Kano

“Ina so ‘yan Najeriya su fahimta cewa muna cikin wani mawuyacin hali. Idan ka yi tafiya zuwa ƙasashen waje da fasfo ɗin Najeriya mai kore, kuma ka tsaya a layi tare da sauran mutane, za ka lura cewa da zarar ka miƙa fasfo ɗin, jami’an shige da fice za su dube ka da wani irin shakku. Idan ma ba su ɗauke ka gefe domin yin bincike na musamman ba. Wannan babban abin kunya ne da wasu matasa ‘yan Najeriya suka jawo mana.”

Ya ci gaba da cewa:“Ina yawan fita don mu’amala da takwarorina da sauran hukumomin gwamnati a ƙetare wajen binciken kuɗaɗe da dawo da kadarori. Kuma akwai abubuwan da ba za ka iya karewa ba. Mun kama wasu gungun matasa kwanan nan, kuma mutane sun daina gaskatawa da aiki tukuru. Ni daga jihar da ilimi ke da daraja nake. Idan ka je makarantar sakandare da na halarta, tun kafin ƙarfe 12 na rana ɗalibai sun bar makaranta.”

Da yake karin haske kan miyagun ayyukan ‘yan damfarar, shugaban EFCC ya ce wasu daga cikinsu suna shiga harkar garkuwa da mutane da kuma ta’addanci idan suka kasa samun wadanda za su yaudara.

Leave a Reply