Hukumar shari’a ta shirya kawo karshen kwacen Waya a Kano

0
177
Hukumar shari'a ta shirya kawo karshen kwacen Waya a Kano

Hukumar shari’a ta shirya kawo karshen kwacen Waya a Kano

Daga Shafaatu Dauda Kano

Hukumar Shari’a ta jihar Kano, ta ce za ta tunkari matsalar ƙwacen Waya tare da haɗin gwiwa da dukkan shugabannin kasuwannin wayoyi da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro da hukunci a jihar Kano, don kawo ƙarshen matsalar.

Kwamishina na biyu a hukumar Shari’a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗan Abba, ne ya bayyana hakan a shafin sa na sada zumunta a ranar Asabar, biyo bayan yadda ake ci gaba da fuskantar ƙalubalen ƙwacen waya a birnin Kano, lamarin da ke sanadiyyar rayukan jama’a daga masu ƙwacen wayar, tare da asarar dukiyoyi.

Sheikh Ali Ɗan Abba, ya kuma ce, a makon da za a shiga ne Hukumar shari’a ta jihar Kano, za ta bayyana irin tsauraran matakan da za ta ɗauka a kan wannan masifar da ta gallabi al’ummar jihar, wato matsalar fashin Waya da Makami.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NEDC ta ƙaddamar da Makarantar Mega ta zamani a Potiskum (Hotuna)

Jaridar Neptune prime, ta ruwaito cewa, Sheikh Ɗan Abba, ya kuma yi addu’a akan lamarin, inda ya ce “Allah ya taimake mu ya kawo mana ƙarshen wannan masifar ta fashin Waya da makami a Kano”.

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’ummar Kano, da masana harkokin tsaro, ke ci gaba da kiraye-kiraye ga mahukunta da su ƙara tashi tsaye wajen yin abinda ya dace don kawo ƙarshen ƙwacen waya, da faɗan Daba, da kuma shaye-shayen kayan maye, a jihar, la’akari da yadda lamarin ya ke damun jama’a.

Leave a Reply