An samu mutuwar Yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Kano sakamakon hatsarin mota

0
104
Rahotanni sun tabbatar da Mutuwar Yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Kano sakamakon hatsarin mota a ciromawa

An samu mutuwar Yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Kano sakamakon hatsarin mota 

Daga Jameel Lawan Yakasai

Tawagar jihar Kano da suka halarci gasar wasanni ta ƙasa National Sports Festival, da aka gudanar a jihar Ogun, sun yi hatsari a karamar hukumar Kura, a hanyar dawowar gida Kano, bayan kammala gasar.

Rahotanni sun bayyana cewa tuni wasu daga cikinsu suka rasu, yayin da aka garzaya da sauran zuwa babban asibitin karamar hukumar Kura.

KU KUMA KARANTA:Hatsarin mota ya kashe mutane 5 ‘yan gida ɗaya a Kano

Daya cikin wadanda ya tsallake rijiya da baya ya tabbatarwa da Jaridar Neptune Prime Hausa cewa Motar da tayi hatsarin na dauke da mutum akalla 35.

Hatsarin ya faru ne bayan da motar ta fada kasan wata gada.

Rahotanni sun tabbatar da rasuwar mutane 20 daga cikin tawagar jihar Kano, da suka gamu da hatsari, a hanyarsu ta dawo wa gida, bayan halartar gasar wasanni ta ƙasa National Sports Festival, da aka gudanar a jihar Ogun.

Hatsarin ya faru ne a safiyar asabar din nan, bayan motar da suke ciki mai dauke da mutane 35, ta fada kasan wata gada a garin Daka Tsalle daga ƙaramar hukumar Kura.

Leave a Reply