Matakin Gwamnatin Nijar na barazana ga kasuwancin mu na dabbobi – AUFCDN

0
153
Matakin Gwamnatin Nijar na barazana ga kasuwancin mu na dabbobi – AUFCDN

Matakin Gwamnatin Nijar na barazana ga kasuwancin mu na dabbobi – AUFCDN

Daga Shafaatu Dauda Kano

Kungiyar Masu fataucin dabbobi da kayan abinci ta Najeriya (AUFCDN) reshen jihar Plateau, ta bayyana matakin da gwamnatin Nijar ta dauka na hana shigo da dabbobi Najeriya musamman raguna, a matsayin abinda ke barazana ga kasuwancinsu na dabbobi a wannan lokaci da ake hada-hadar babbar Sallah ta wannan shekara.

Shugaban Kungiyar na jihar Plateau, Alhaji Musa Bamban, ne ya bayyana hakan a yayin zantawarsa da Manema labarai inda ya ce yanzu haka suna cikin fargaba a sakamakon ɗaukar wannan mataki.

A cewar Bamban, “Yanzu haka mutanen mu suna cikin fargaba a sakamakon matakin gwamnatin Jamhuriyar Nijar, la’akari da yadda matakin yake barazana ga harkokin kasuwancin dabbobi a wannan lokaci da bikin babbar Sallah ke kara karatowa”.

KU KUMA KARANTA:Nijar ta dakatar da fitar da dabbobi zuwa ƙetare a gabanin sallah

Haka kuma ya alakanta matakin a matsayin abin da zai haifar da karancin dabbobin da tsadar su, a sakamakon matukar bukatar da ake da ita a wannan lokaci da ake bikin babbar sallar wanda ake yin “Layya”.

Ya kara da cewa yanzu haka suna jiran su ji sakamakon tuntuɓar da uwar kungiyar su ta yi dangane da lamarin, duba da cewa sun san shugaban su na kasa, Kwamared Muhammad Tahir jajirtacce ne akan abinda ya shafi matsalolin mutanen da yake jagoranta.

A ƙarshe ya yi fatan mahukuntan Jamhuriyar Nijar za su sake duba lamarin, domin samar da maslaha ga masu kasuwancin dabbobin a kasashen biyu dama a’ummomin su domin yiwa tufkar hanci.

Leave a Reply