Za a gina birnin Dawakai ma fi girma na farko a Katsina

0
153
Za a gina birnin Dawakai ma fi girma na farko a Katsina

Za a gina birnin Dawakai ma fi girma na farko a Katsina

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamnatin Jihar Katsina ta samu amincewa daga Hukumar Wasanni ta Kasa domin gina Birnin Dawakai na farko a nahiyar Afirka, bayan wata muhimmiyar ganawa tsakanin Gwamna Dikko Umaru Radda da Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa, Malam Shehu Dikko.

An kulla wannan gagarumin aikin wanda kudinsa ya kai biliyoyin naira, a wata hadakar ganawa da ta hada da Ministar Harkokin Al’adu, Yawon Bude Ido da Tattalin Arzikin Kirkira, Barr. Hannatu Musa Musawa; Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa, Malam Shehu Dikko da Daraktan Hukumar Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Katsina, Dr. Kabir Ali Masanawa.

Gwamna Radda ya bayyana cewa, aikin Birnin Dawakai zai kara inganta kokarin gwamnatin jihar na raya al’adun jihar Katsina tare da samar da hanyoyin tattalin arziki masu dorewa ga al’ummar jihar da arewacin Najeriya gaba daya.

KU KUMA KARANTA:A Azare, ƙungiyoyi sun yi ƙira ga mahukunta da su dakatar da hawa Dawakai a lokacin bukukuwa

Sabon birnin na zamani zai kunshi manyan wuraren gudanar da bikin Durbur, filayen tsere na dawaki, makarantar horar da wasannin dawaki (Equestrian Academy), kulob din Polo, da kuma hedikwatar wasannin dawakai na kasa da kasa na farko a yammacin Afirka.

Baya ga haka, aikin zai hada da gine-ginen zamani irin su Villas da Duplexes da za su nuna kyawawan al’adun Arewa.

“Jagorancin hangen nesa na Gwamna Radda ya kai mu ga wannan muhimmin aiki da zai samar da dubban ayyukan yi tare da mayar da Katsina zuwa cibiyar kasa da kasa ta wasannin dawakai,” in ji Dr. Masanawa, jim kadan bayan samun amincewar aikin.

Leave a Reply