An samu raguwar hauhawar Farashi da kaso 23.71 a Najeriya – NBS

0
209
An samu raguwar hauhawar Farashi da kaso 23.71 a Najeriya - NBS

An samu raguwar hauhawar Farashi da kaso 23.71 a Najeriya – NBS

Daga Shafaatu Dauda Kano

An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya daga kashi 24.23 a watan Maris ɗin 2025 zuwa kashi 23.71 a watan Afrilun 2025.

Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta ce hauhawar farashin da aka samu a watan Afriliu ya nuna an samu ragin kaso 0.52 na hauhawar idan aka kwatanta da watan Maris.

KU KUMA KARANTA:Tattalin arziƙin Najeriya ya bunƙasa da kaso 3.84 cikin 100 a zango na 4 na 2024 – NBS

“Wannan na nuni da cewa hauhawar farashin Ta shekara-shekara Ta ragu a watan Afrilun 2025 idan aka kwatanta da watan Afrilun 2024.”

Dangane kuma da hauhawar farashin kayan abinci a watan Afrilun 2025 ta kasance kaso 21.26 kamar yadda ke faruwa a shekara-shekara.

Leave a Reply