Masu ƙwacen waya a Kano sun kashe ɗalibin Jami’ar Bayero
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Masu ƙwacen waya sun kashe wani ɗalibi da ke karatu a Jami’ar Bayero a Unguwar Ɗanɓare.
Ɗalibin Mai suna Usman Dan asalin kasar Niger ya rasa ran nasa ne daidai lokacin wadannan barayi suka shiga wannan unguwa da zummar kwacen waya.
KU KUMA KARANTA:Zargin satar Kare, an kashe wani mutum a Bauchi
A cewar kwamandan vigilante na yankin Abubakar Lawan yace lamarin ya farune bayan sallah asuba Kuma ana zargin barayin sun kashe matashin ne ta hanyar kacha Masa makamin Danbuda tare karbe wayoyin wasu daliban guda Hudu.
Kan wannan batu, mun tuntubi kakakin rundunar yan sadan jihar kano SP Abdullahi Haruna kiyawa wanda har zuwa wannan lokacin baice komai ba Alabasshi idan ya magantu zaku jimu dashi.









