Jami’ai daban-daban na ta ƙoƙarin kashe gobarar da ke ci ba ƙaƙƙautawa a Isra’ila
Daga Ibraheem El-Tafseer
Fiye da tawagogi 150 da jiragen kashe gobara na ci gaba da kashe wutar da ta tashi a gobarar da ake kallo a matsayin mafi muni a tarihin Isra’ila.
Wutar na ƙara ruruwa sakamakon kaɗawar iska mai ƙarfi da ƙaruwar yanayin zafi.
Hukumar kashe gobara ta ƙasar ta ce ta samu nasarar kashe ɗaya daga cikin gobarar dajin da ta tashi a yankin Birnin Ƙudus.
KU KUMA KARANTA:Ana ci gaba da musayar fursinoni tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hamas
Firmainistan ƙasar, Benjamin Netanyahu wanda tuni ya ayyana gobarar da matsalar gaggawa ta ƙasa, ya ce an kama mutum takwas bisa zargin hannu a tashin gobarar.
To sai dai ‘yansanda sun ce mutum uku kawai aka tsare, kuma dalilin tsare su ba shi da alaƙa da tashin gobarar.









