Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da bincike kan matsalolin ruwansha a jihar

0
47
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da bincike kan matsalolin ruwansha a jihar

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da bincike kan matsalolin ruwansha a jihar

Daga Shafaatu Dauda Kano

Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin, Injiniya Abba Kabir Yusif, ta ƙaddamar da bincike kan matsalolin samar da kyakkyawan Ruwan sha da kuma na Noman Rani a ƙananan hukumomin jihar goma sha takwas (18).

Hukumar Bincike da adana muhimman bayanai ta jihar ce ta ƙaddamar da binciken da nufin gano musabbabin waɗannan matsaloli da kuma samo hanyoyin warware su don inganta samar da ingantaccen ruwan Sha da na noman Rani domin haɓɓaka amfanin gona.

Da take ƙaddamar da kwamitin binciken a jiya Alhamis, Babbar Daraktar hukumar, Hajiya Nana Asma’u Jibrin, ta jaddada ƙudirin Gwamnan Kano na tabbatar da cewa an samar da tsaftataccen ruwa mai inganci ga ɗaukacin yankunan jihar.

Ta kuma bukaci ma’aikatan sashen, musamman waɗanda ke jagorantar wannan bincike, da su tabbatar da ziyartar dukkanin sassan ƙananan hukumomin da abin ya shafa domin tattara sahihan bayanan da za su taimaka wajen shawo kan waɗannan matsaloli cikin ƙanƙanen lokaci.

KU KUMA KARANTA:Matsalar ruwan sha a Warawa ta jihar Kano, har ya kai ga suna shan ruwan da Karnuka ke Wanka

A cewar ta, “Manufar binciken shine don fahimtar matsalolin da suka haifar da matsalar a waɗannan kananan hukumomi, ta yadda sakamakon binciken zai bayar da shawarwari da dabarun tsara manufofin da za su inganta tsarin samar da ruwa, bunƙasa noman zamani, da kuma tabbatar da isasshen abinci a faɗin jihar”.

Sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Rabiu Umar Isah, ya aiko wa jaridar Neptune prime Hausa ta ce kwamitin binciken na ƙarƙashin Daraktan bincike na hukumar Malam Mustapha Sadi da kuma takwaransa na ƙididdiga da tsare-tsare, Malam Abdulkarim A. Ibrahim.

Ƙananan hukumomin da wannan bincike ya shafa sun haɗa da Gaya, Rano, Nasarawa, Shanono, Minjibir, Dawakin Kudu, Bebeji, Tsanyawa, Garin Malam, Karaye, Bichi, Gezawa, Ungogo, Kiru, Bagwai, da Albasu, Ghari da kuma tarauni.

A ƙarshe ta jaddada ƙudirin Gwamnatin jihar na magance matsalolin da ke addabar fannin noman jihar, ciki har da rashin ingantattun hanyoyin ban ruwa da kuma ƙarancin hanyoyin samun kuɗaɗe, don inganta rayuwar al’umma da kuma tabbatar da ci-gaba mai ɗorewa a lungu da saƙo na jihar.

Leave a Reply