No menu items!

Sample Page Title

Date:

‘Yansanda a Kano, sun gayyaci Shamakin Kano kan zargin saɓa wa umarnin haramta hawan sallah a jihar

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Rundunar ƴansandan jihar Kano ta gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku domin amsa tambayoyi kan zargin saɓa wa umarnin da ƴansandan suka bayar na haramta Hawan Sallah a Kano.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce rundunar ta jaddada matsayinta na haramta Hawan Salla a faɗin jihar, kuma duk wanda aka samu da laifin saɓa umarnin zai ɗanɗana kuɗarsa.

Kwanaki kafin ranar Sallah ne dai rundunar ƴansandan jihar ta fitar da sanarwar haramta Hawan Sallah a Kano bayan da ta ce ta samu bayanan sirri na wasu ɓata-gari da ke da aniyar haifar da tashin hankali a lokacin hawan.

KU KUMA KARANTA:Rundunar ‘yansanda ta hana hawan Sallah a Kano

Haka kuma sanarwar ta ce kwamishinan ƴansandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya kafa wani kwamitin ƴansanda mai mambobi takwas domin gudanar da bincike kan tashin hankalin da aka samu a ranar Sallah lokacin da tawagar Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi ke komawa gida bayan jagorantar Sallar Idi.

A lokacin da aka samu hatsaniyar dai an kashe wani jami’in sintiri tare da raunata wani da ke aikin bayar da tsaro ga tawagar sarkin Kano Mal Sanusi Lamido Sanusi.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...