An dawo da mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars Abdallah, bayan dakatar da shi
Daga Jamilu Lawan Yakasai
A kwanakin baya ne kocin ya tanka wa magoya bayan Pillars din da su ka nuna ɓacin ran su a wani wasa da ƙungiyar ta yi ba ta samu nasara ba a filin wasa na Sani Abacha, lamarin da ya sa mahukunta su ka dakatar da shi.
KU KUMA KARANTA:Abin da ya sa aka dakatar da mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars
Sai dai a safiyar yau Talata, kungiyar ta sanar da dawowar kocin a shafin ta na X, inda ta ce duk wata matsala an warware ta, kuma yanzu haka zai ci gaba da jan ragamar kungiyar har zuwa ƙarshen kakar wasanni ta bana.









