Kotun ɗaukaka ƙara ta dakatar da aiwatar da hukuncin da ta yi kan rikicin Masarautar Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
A wani sabon salo kan rikicin Masarautar Kano, Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin da ta yanke a ranar 10 ga Janairu, wanda ya tabbatar da rushewar Dokar Majalisar Masarautar Kano ta 2019 da Gwamnatin Jihar Kano ta yi. Wannan dakatarwar za ta kasance har zuwa lokacin da Kotun Koli za ta yanke hukunci kan karar da aka daukaka.
A baya, Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin da Mai Shari’a Abubakar Liman na Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ya yanke a ranar 20 ga Yuni, wanda ya soke duk matakan da Gwamnatin Kano ta dauka bisa Dokar Soke Majalisar Masarautar Kano ta 2024. Wadannan matakai sun hada da rushe sababbin masarautu da kuma mayar da Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16. Kotun Daukaka Kara ta yanke hukunci cewa Mai Shari’a Liman ya wuce huruminsa wajen soke wadannan matakai.
KU KUMA KARANTA:Kotu ta haramta wa Aminu Ado Bayero ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano
Kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari’a Okon Abang ne suka yanke hukunci kan bukatar dakatarwar a ranar Juma’a.
Alhaji Aminu Babba DanAgundi (Sarkin Dawaki Babba) ne ya shigar da kara kan Gwamnatin Jihar Kano, Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Hukumar Tsaro ta NSCDC, da wasu hukumomin tsaro.