Ba za mu tattauna da Amurka kan dakatar da shirin nukiliya ba – Khamenei

0
20
Ba za mu tattauna da Amurka kan dakatar da shirin nukiliya ba - Khamenei

Ba za mu tattauna da Amurka kan dakatar da shirin nukiliya ba – Khamenei

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jagoran addini na jamhuriyar Musulunci ta Iran Ayatollah Ali Khamenei, ya yi watsi da buƙatar Shugaban Amurka Donald Trump ta neman ƙasar Iran ta buɗe ƙofar tattaunawa domin dakatar da shirinta na samar da makamin nukiliya.

Khamenei ya ce Iran ba za ta shiga tattaunawa ba domin matsin lamba daga ƙasar da ya bayyana da “mai raini da wulaƙanci.”

KU KUMA KARANTA:Ba za mu yi sulhu da Amurka ba – Ayatullah Ali Khamene’i

A shekarar 2018 ce Trump ne fice daga yarjejeniyar rage wa Iran takunkuman da aka ƙaƙaba mata, wanda aka yi domin a rarrashe ta ko hakan zai sa ta fara nazarin dakatar da shirin nata na nukilya.

Sai dai bayan wannan matakin Iran ɗin ta ci gaba da sarrafa uraniun ɗinta, wanda a yanzu ya kusa kai matakin makamin na nukiliya.

Leave a Reply