Za mu yiwa filin jirgin saman Legas ginin zamani – Ganduje
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Shugaban kwamitin Daraktoci na Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama na Ƙasa (FAAN), Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya jaddada bukatar gyara na gaggawa a filin sauka da tashi na jirgin sama dake Murtala Muhammed (MMIA) a cewar sa, ya fara zama tsohon yayi.
KU KUMA KARANTA:Kotu ta da ɗage sauraron ƙarar Abdullahi Ganduje kan zargin badaƙalar kuɗaɗe
Yayin ziyarar gani-da-ido ta farko da ya kai MMIA, tare da rakiyar Manajan Daraktan FAAN, Misis Olubunmi Kuku, Ganduje ya tabbatar da cewa yawancin kayan aikin filin jirgin saman sun tsofa wasu kuma sun lalace.
Ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki tabbacin cewa kwamitin zai hada kai da hukumar ta FAAN domin gyara filin jirgin da zamanantar da shi, wanda zai yi daidai da yadda filayen jiragen sama su ke a faɗin duniya.