Fitaccen ɗan siyasa a Kano, Alhaji Ahmadu Zago ya rasu

0
14
Fitaccen ɗan siyasa a Kano, Alhaji Ahmadu Zago ya rasu

Fitaccen ɗan siyasa a Kano, Alhaji Ahmadu Zago ya rasu

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Fitaccen ɗan siyasa kuma shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano, Ambasada Haruna Zago ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan hukumar ne ya shaidawa manema labarai rasuwar Dan Zago ɗin a yau Alhamis.

KU KUMA KARANTA:Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano ta kama wasu jami’an gwamnatin jihar kan zargin ɓatan naira miliyan 105

Ya ce za a yi jana’izarsa a gidan sa da ke Kurna, Tudun Bojuwa, kusa da Kunya Chemist a yau Alhamis da misalin ƙarfe 1 na rana.

Ɗan Zago dai fitaccen ɗan siyasa ne a jihar Kano, wanda da shi aka riƙa yaƙin neman zaɓen tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

A ranar 5 ga watan Yulin 2023 ne Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa Haruna Zago a matsayin Shugaban hukumar kwashe shara ta Kano.

Leave a Reply