Mulki ba zai koma arewa ba sai Tinubu ya kammala shekaru 8 – Abdullahi Ganduje

0
183
Mulki ba zai koma arewa ba sai Tinubu ya kammala shekaru 8 - Abdullahi Ganduje

Mulki ba zai koma arewa ba sai Tinubu ya kammala shekaru 8 – Abdullahi Ganduje

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa sai shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kammala shekaru takwas na mulki kafin ƴan Arewa su karba, nan da 2031.

Hakan na zuwa ne bayan rahotanni ke cewa wasu ‘yan arewa na shirin haɗa maja don kawo ƙarshen mulkin na Tinubu a 2027.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Ganduje ya baiyana haka ne a jiya Talata a birnin Abuja yayin da ya karbi bakuncin wata tawaga ta Kungiyar Matasa masu goyon bayan Tinubu daga Arewa.

KU KUMA KARANTA:Ina ƙira ga ‘yan Najeriya a ƙara haƙuri da Tinubu – Ganduje

Yayin da ya ke yabawa kungiyar bisa tsara manufofinta da kuma samar da muhimman bayanai kan zabe, Ganduje ya ce APC tana shirye ta ba ta dukkan goyon bayan da take bukata.

“Mu na ganin shirinku na yadda za ku tara masu zabe dangane da zaben 2027. Wannan abin karfafa gwiwa ne. Dole ne in taya ku murna kan wannan. Haka kuma, kun sani, shugabanmu na arewa ne, shugabanmu na kudu ne, shugabanmu na yankuna shida ne a ƙasar nan kuma muna karɓar kungiyoyin goyon baya daga dukkan yankuna shida.

“Muna farin ciki cewa jam’iyyarmu tana goyon bayan tsarin karba-karba na mulki. Lokacin da shugaba daga yankin arewacin wannan kasa ya yi shekaru takwas a kan mulki, mun tsaya kan cewa shugaban kasa na gaba daga jam’iyyarmu ya fito daga kudu, kuma da yardar Allah, mun yi aiki tukuru tare da hadin kan ‘yan Najeriya.

“Shugabanmu ya fito daga kudu kuma yana shirin yin wa’adi na biyu a 2027, da yardar Allah. Bayan haka kuma, mulki zai koma yankin Arewa,” in ji Ganduje.

Leave a Reply