Ba za mu yi sulhu da Amurka ba – Ayatullah Ali Khamene’i

0
77
Ba za mu yi sulhu da Amurka ba - Ayatullah Ali Khamene'i

Ba za mu yi sulhu da Amurka ba – Ayatullah Ali Khamene’i

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jagoran addini a jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya yi ƙira ga gwamnatin ƙasar da ka da ta ”kuskura” ta yi tattaunawar sulhu da Amurka, yana mai cewa yin hakan ganganci ne.

A taron da ya yi da shugabannin sojin ƙasar, Ayatollah ya ce gwamnatin Trump mai ruguzawa tare da saɓa wa yarjejeniyoyin da aka ƙulla ne.

KU KUMA KARANTA:Sinwar tsayayyen ɗan gwagwarmaya ne – Khamene’i

Ya yi gargaɗin cewa magana da gwamnatin irin wannan ba alheri ba ne inda ya ce idan suka yi musu barazana toh za su mayar da martani.

”Idan kuma suka ce mana kule, to za mu ce musu cas”, in ji jagoran addinin.

A farkon makon nan ne shugaba Trump ya nemi a samar da ingantaciyyar yarjejeniyar makamin nukiliya da Iran wadda a ƙarƙashinta za a hana ta ƙera makaman nukliya ɗin.

Leave a Reply